Shugaban hukumar NYSC Burgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu, ya tabbatar da cewa za’a fara biyan masu hidimtawa ƙasa alawus ɗin Naira dubu 77 a ƙarshen watan Maris.
Ana kyautata zaton Gwamnatin tarayya zata kashe kuɗin da yakai Naira biliyan 430.7, a lokacin da za’a fara biyan sabon alawus ɗin, da aka canja daga Naira dubu 33 zuwa dubu 77.
An dai jima ana cewa za’a fara biyan sabon alawus ɗin amma abin yaci tura, tun lokacin da gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
Ko a makon daya gabata sai da wata ƴar hidimar kasa a jihar Lagos mai suna Ushei Uguamaye, ta caccaki shugaban ƙasa Tinubu akan cewa tana cutuwa da tsarin NYSC bisa hujjar cewa kuɗin da ake biyan ta sun yi kaɗan wajen gudanar da rayuwa a wata, saboda tsadar kayan masarufi.