Majalisar dattawa ta amince da dokar ta ɓacin jihar Rivers

0
33

Majalisar dattawa ta amincewa shugaban ƙasa Tinubu ya ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Rivers.

Majalisar ta amincewa bukatar shugaban ƙasar lokacin da ta gudanar da wani zaman sirri a yau Alhamis.

Tuni itama majalisar wakilai ta sanar da yarjewa Tinubu sanya dokar bayan da mafi yawan mambobin majalisar suka bayyana amincewa da dokar da kuma sanya gwamnan riƙon ƙwarya a Rivers.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here