An fara shirya yadda za’a yiwa Sanata Natasha kiranye daga majalisar dattawa don tsige ta daga kujerar ta.
Natasha dai ta kasance mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, da take fuskantar kalubale iri iri bayan da ta zargi shugaban majalisar dattawa Akpabio da yunƙurin lalata da ita.
Tuni dai kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa wasu daga cikin yankunan da Natasha ke wakilta sun fara yi shirin yi mata kiranye akan hujjar cewa basu da kwarin gwuiwa akan ta saboda rikicin dake faruwa da ita a majalisa da yasa aka dakatar da ita.
NAN yace an fara shirin a yau Laraba, inda aka faro daga Lokoja babban birnin jihar Kogi, sai Ajaokuta, Adavi, Okene, da ƙaramar hukumar Okehi.
Wasu daga cikin al’ummar yankunan sun taru a mazaÉ“un su tare da kaÉ—ai mata Æ™uri’ar yanke Æ™warin gwuiwa kamar yadda wani mai suna Abdullahi Usman, ya bayyanawa NAN.