Wata gobara mai girma ta ƙone kasuwar ƴan gwangwan ta Dakata, kusa da wani gidan mai dake Zango Road a ƙaramar hukumar Nasarawa dake jihar Kano.
Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa wutar ta fara ci a yankin kwalema a hanyar Zango dake kusa da gidan mai na Dominion daura da ofishin hukumar WAEC na Kano.
Zuwa yanzu ba’a gano dalilin tashin gobarar ba da adadin asarar da akayi.