Shugaba Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a Rivers tare da dakatar da gwamnan jihar Siminalaya Fubara da mataimakiyar sa, haɗi da mambobin majalisar dokokin jihar tsawon watanni 6, sakamakon rikicin siyasar da yaƙi ci yaƙi cinyewa.
Tinubu ya kuma naɗa Vice Admiral Ibok Ibas, mai ritaya a matsayin gwamnan Rivers na riƙo.