Shugaban Amurka Donald Trump ya gana da takwaransa na Rasha Vladmir Putin a yau Talata.
:::Hisbah ta kama Ummin Mama Ba mai yi, yar TikTok
Shugabannin sun gana ta wayar tarho dangane da yadda za’a shawo kan yakin Rasha da Ukraine wanda aka shafe lokaci mai tsawo ana gwabzawa.
Fadar gwamnatin Amurka White House, tace manufar tattaunawar shine a samar da tsagaiwa wuta a yakin kasashen Rasha da Ukraine, tare da cewa akwai alamun nasara a yunkurin sulhun.
Yakin Rasha da Ukraine dai ya haifar da mummunar asara ga kasashen biyu musamman ma Ukraine wadda Rasha tafi samun galaba akan ta duk da cewa kasashen Amurka da turai na bata taimakon kayan yaki.
Bayan haka yakin ya haifar da tsadar tsadar hatsi a sassan duniya da kuma tsadar makamashi.