An ƙona bututun Man fetur a jihar Rivers mai fama da rikicin siyasa

0
42

An samu tashin wuta a bututun danyen man fetur daya ratsa ta yankin Neja Delta a Bodo dake karamar hukumar Gobana ta jihar Rivers, wanda hakan ya haifar da fargabar ko an kai harin da gangan.

Zuwa yanzu ana kan gudanar da bincike don gano cewa ko tsageru ne suka kai harin a daren Litinin, biyo bayan barazanar harin da suka yiwa gwamnatin tarayya na cewa zasu kai hari kan bututun Man in har aka rike kason kudin Rivers daga asusun gwamnatin tarayya, saboda hukuncin kotun koli.

Kotun ta bayar da umarnin ne sakamakon rikicin siyasar da jihar ke ciki tsakanin yan majalisar dokokin jihar masu goyon bayan ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, da gwamna Siminalaya Fubara.

Bututun Man da aka ƙone shine ke jigilar danyen mai zuwa Bonny, wanda aka bayar da rahoton cewa mahukunta na kokarin shawo kan wutar take ci a jikin bututun, da Kuma sanin adadin asarar da hakan ya janyo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here