Ba’a baiwa ko waca jaha damar mallakar makamai masu sarrafa kansu ba – Fadar Shugaban Kasa

0
102

Fadar shugaban kasa ta ce babu wata jiha a cikin tarayya da aka ba ta izinin sayo makamai masu sarrafa kansu don jamiā€™an tsaro.

Malam Garba Shehu, mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata a Abuja, ya yi watsi da rahotannin cewa an baiwa gwamnatin jihar Katsina lasisin sayo da sarrafa makamai masu sarrafa kansu.

A cewarsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha bayyana karara cewa babu wanda aka yarda ya dauki AK-47 ko wani makami ba bisa ka’ida ba, kuma dole ne ya mika shi.