Kungiyar Kristoci zata yiwa gwamna Uba Sani addu’ar samun nasara

0
63

Kungiyar Kristoci ta kasa CAN reshen jahar Kaduna tace zata yiwa gwamna Uba Sani, addu’ar samun nasara.

Shugaban kungiyar Rabaran Celeb Ma’aji, ne yayi alkawarin gudanar da addu’ar inda yace ba zasu manta da karramawar da Uba Sani, yayi musu ba na shigar dasu cikin harkokin gwamnatin sa.

Ma’aji ya jinjina wa gwamnan na Kaduna akan tsare tsaren gwamnatin sa, musamman yadda yake bawa kowanne bangare dama don samar da cigaban jihar.

Shugaban Kristocin ya sanar da hakan a jiya lahadi lokacin da yayi buÉ—a baki tare da Uba Sani, a gidan Kashim Ibrahim.

Celeb, yace tabbas akwai banbancin shugabanci tsakanin gwamnatin El-Rufa’i da Uba Sani, musamman yadda yake bawa Kristoci dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here