Mai gudanar da Fim din Batsa ta karɓi addinin muslinci

0
161

Kae Asakura, wadda aka fi sani da Rae Lil Black, ta dena aikata laifin Fim din Zina tare da komawa addinin muslinci.

Asakura ta kasance yar asalin kasar Japan, da ta shiga muslinci a kasar Malaysia.

Rahotanni sun bayyana cewa halayyar karamcin da musulmai suka nuna mata a Malaysia ta taka muhimmiyar rawa wajen janyo ra’ayin ta zuwa addinin.

A kasar ta Malaysia an bayyana cewa Asakura ta dena saka kananun kaya, tare da yin azumin watan Ramadan.

Bayan shiga muslinci Asakura ta fito shafin sada zumunta tare da bayyanawa duniya cewa yanzu ita musulma ce, wanda Musulmai da dama suka yi mata fatan alkairi, da kuma bata kyautuka cikin su har da littattafan addinin muslinci.

Ta kuma bayyana dana sani akan laifin yin fim din Batsa da tayi a baya, inda tace a yanzu bata da ikon hana mutane wallafa tsaffin bidiyon da tayi mara kyau, sannan tace zata mayar da hankali akan sabuwar rayuwar data shigo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here