Idan za’a iya tunawa dai rikicin diflomasiyya ya kunno tsakanin kasashen Afrika ta Kudu da Amurka, inda shugaba Trump, ya zargi gwamnatin Ramaphosa da kwace kadarorin Amurkawan dake zaune a Afrika ta Kudu.
Kadarorin sun kunshi gonaki da filaye, sai dai gwamnatin Afrika ta Kudu ta musanta zargin da Amurka tayi.
Ko a kwanakin baya sai da shugaban Amurka Donald Trump, yace zai bawa manoman Afrika ta Kudu damar zama a Amurka in har tsoron zaman kasar saboda barazanar gwamnati.
Wannan rikicin shine dalilin korar jakadan bayan Amurka ta zarge shi da kalubalantar Trump.