Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, yace a shirye yake domin yin tafiyar da zata kawowa Najeriya kyakyawan shugaban tare da Peter Obi.
Bala Muhammad, ya bayyana hakan a yau Alhamis lokacin da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar LP a shekarar 2023 Peter Obi, ya kai masa ziyara a gidan gwmanatin jihar Bauchi.
Yace shi da Peter Obi, sun gana akan yadda za’a magance matsalolin talauci da aikata laifuka a Najeriya.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa zai hada kai da Obi wajen samar da shugabanci mai kyau a kasar nan. Sannan yace duk gwamnonin PDP suna da irin wannan manufa ta kawo gyara a Najeriya.
A nasa jawabin Peter Obi, cewa yayi bayanin cewa manufar yin ziyarar tasa itace ya zanta da gwamna Bala Muhammad, akan matsalolin da kasar nan ke ciki, saboda yana daga cikin masu ruwa da tsaki a kasa sannan shine shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP.
Obi, ya kara da cewa daga cikin abubuwan da suka zanta akwai kalubalen da arewa ke fama dasu.