Trump zai kara harajin kaso 200 akan giyar da ake kaiwa Amurka daga Turai

0
138
Donald Trump
Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi barazanar ƙarin harajin kashi 200 akan giyar da ake shigarwa Amurka daga kasashen nahiyar Turai.

Trump ya yi barazanar ce bayan da ƙasashen Turai da Canada suka yi alƙawarin mayar da martani ta hanyar lafta haraji kan kayyakin Amurka bayan da shugaban na Amurka ya sanya ƙarin harajin kashi 25 kan ƙarafan da ake shiga da su ƙasarsa.

A lokacin da yake jawabi ga manema labarai a fadar White House kan barazanar ƙasashen, Trump ya ce idan kasashen Turai suka ɗorawa Amurka ƙarin haraji, shima zai lafta musu harajin.

Trump yace harajin da zai jibgawa barasa sai ya fi muni da ƙarin kashi 200 domin mayar da martani.

Tuni dai hannayen jarin kamfanonin sarrafa basara suka faɗi sakamakon kalaman na Trump.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here