Gwamnatin Amurka ta sanar da shirin da take yi na korar kaso 50 cikin dari na yawan ma’aikatan fannin Ilimin kasar, a daidai lokacin da gwamnatin Trump ke aiwatar da sabbin manufofin tattalin arziki.
Ma’aikatar Ilimin tace rage ma’aikatan ya zo a yayin da shugaban kasar ke kokarin ganin ya rage yawan ma’aikatan da gwamnatin tarayyar Amurka ke dasu.
Sakatariyar harkokin ilimi Linda McMahon, tace rage ma’aikatan zai shafi kowanne bangare na Ilimin Amurka sannan za’a ga canje canje a wasu bangarorin.
Zuwa yanzu an turawa ma’aikatan sako ta shafin karÉ“ar sakonni na email cewa a yau Laraba kar su fito aiki saboda shirin da akayi na rufe ofisoshin ma’aikatar Ilimin.