Cutar sankarau ta barke a jihar Kebbi, zuwa yanzu ta hallaka Mutane 26.
Gwamnatin jihar ce ta tabbatar da barkewar cutar ta sankarau a kananun hukumomi guda uku.
Kananun hukumomin da aka samu cutar sun kunshi Aliero, Gwandu da Jega.
Cutar sankarau dai na da illa sosai ga rayuwar dan Adam, musamman yadda take nakasa wanda ta kama wani sa’in ma tayi ajalin mutum baki daya.