Jam’iyyar APC ta nemi a tsige gwamnan jiihar Rivers

0
51

Jam’iyyar APC reshen Rivers ta nemi gwamnan jihar Siminalaya Fubara, ya sauka daga mukamin sa ko kuma a tsige shi.

APC ta bayyana hakan a matsayin mayar da martani ga gayyatar da Fubara ya yiwa yan majalisar dokokin jihar 27 masu goyon bayan ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, don yin liyafar cin abinci a yau litinin.

:::NNPCL ya dena siyarwa matatar Dangote danyen man fetur

Shugaban APC, na jihar Tony Okocha, ne ya bayyana hakan tare da kalubalatar gayyatar da Fubara ya yiwa yan majalisar 27.

Okocha, yace sau da dama Fubara, ya nuna kin mutunta shugaban kasa Bola Tinubu, dangane da sasantawar da ya yiwa rikicin sa da Wike, tare da kin yiwa hukuncin kotu biyayya.

Okocha, ya kara da cewa a yanzu gwamnan jihar ta Rivers, bashi da wani zabin daya wuce sauka daga mukamin sa ko kuma a tsige shi, tun da bai yi nasara a kotun koli ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here