Yan bindiga sun kai hari garin Zakirai na karamar hukumar Gabasawa dake jihar Kano, inda suka yi garkuwa da wani matashi Mohammed Bello, ɗan shekara 20, sannan wani mai suna Abubakar ya ji rauni.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen sun kai hari gidan wani mutun mai suna Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda ma’aikaci ne a wani asibiti mai zaman kansa a garin na Zakirai.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an ƴan sanda sun fara neman maharan, Kuma kokarin ceto wanda suka yi garkuwa da shi.