Shugaban Amurka Donald Trump, zai bayar da shaidar zama ɗan ƙasa ga manoman kasar Afrika ta Kudu, dake son barin kasar.
Trump yace cikin gaggawa Amurka zata bawa manoman shaidar zama ɗan ƙasa in har suna son haka.
A kwanakin baya dai an samu tankiya tsakanin Amurka da Afrika ta Kudu, dangane da zargin gwamnatin Ramaphosa da kwacewa turawa gonaki.
Sai dai gwamnatin Pretoria ta musanta zargin Trump da yace ana kokarin kwacewa turawa gonaki a Afrika ta Kudu.
Zuwa yanzu ana fuskantar raunin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.