Za’a bude sabbin matatun fetur a Najeriya

0
78

Hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa NMDPRA ta bawa wasu kamfanoni 3 lasisin buɗe matatun man fetur a Najeriya.

NMDPRA ta sanar da hakan a jiya Juma’a cikin wata sanarwa data fitar a shafin ta na X, inda tace matatun zasu rika tace danyen man fetur da yawan sa yakai ganga dubu 140 a kowacce rana.

Hukumar NMDPRA tace matatar Eghudu, zata rika tace gangar mai mai dubu 100 a rana,  sai matatar MB da zata rika tace gangar mai dubu 30 a rana, yayin da HIS zata tace ganga dubu 10 kowacce rana.

Shugaban hukumar NMDPRA Injiniya Farouk Ahmad, ne ya bayar da lasisin, wanda za’a samar da matatun a jihohin Edo, Abia, da Delta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here