Shugaban kasa Tinubu ya rage kuɗin wankin ƙoda

0
32

Shugaban kasa Tinubu ya rage kuɗin wankin ƙoda a asibitocin gwamnatin tarayya 11, inda aka sanya tallafi a wankin.

Kudin wankin ƙodar zai dawo Naira dubu 12, sabanin Naira dubu 50 da aka saba biya.

Asibitocin da aka yi ragin sun haɗa da Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Tarayya (FMCs) Ebute-Metta Legas, Jabi, Abuja, Asibitin Kwalejin Jami’ar Ibadan (UCH), Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Owerri, da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) Maiduguri.

Sauran sun hada da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Abeokuta, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LUTH) Legas, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Azare, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) Benin, da Jami’ar Koyarwa ta Calabar (UCTH) Calabar.

An kaddamar da tallafin ne a watan Janairu a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

A cewar Hammatu Haruna, manaja mai kula da sashen masu ciwon ƙoda a asibitin koyarwar na Bauchi, tallafin zai kawo sauki ga marasa lafiya, musamman masu ciwon ƙoda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here