Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Neja ta sanar da ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin lokacin gudanar da zaɓen kananun hukumomin jihar.
Shugaban hukumar Injiniya Mohammed Jibrin Imam, ne ya sanar da hakan lokacin da yake bayyana jadawalin yadda zaben zai kasance a Minna.
Yace an fara shirin zaɓen a ranar 6 ga watan Maris da muke ciki, yayin da za’a yi zaɓen fidda gwani a tsakanin ranakun 15 zuwa 25 na watan Maris.
Sannan za’a bayyana wadanda za’a tsayar takarar daga 25 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu.
Imam ya kuma yi alkawarin gudanar da sahihin zaɓe mai cike da adalci ta hanyar yin amfani da ka’idojin da hukumar zaɓen ta gindaya.