Sojoji sun kaiwa ofishin samar da lantarki hari

0
50

Sojojin sun kai hari ofishin lantarki saboda yanke musu wuta a jihar Lagos.

Wasu jami’an sojojin sama da ke sansanin Ikeja a birnin Lagos na Najeriya sun kai hari kan Ofishin Rarraba Wutar Lantarki da ke Ikeja, inda suka yi wa ma’aikatan lantarkin da wani ɗan jarida dukan tsiya.

Rahotanni na cewa, sojojin sun kai harin ne bayan ma’aikatan lantarkin sun katse musu wutar da suke samu a sansaninsu.

Bayanai na cewa, sojojin sun cin zarafin hatta wani ɗan jarida da ke aiki da gidan jaridar Punch, wato Dare Olawin. 

Sansanin sojin saman na Sam Ethnan ya shafe tsawon makwanni biyu cikin duhu ba tare da samun wutar lantarki ba.

RFIHAUSA sun rawaito cewa nn dai yanke wa sansanin wutar lantarkin ne sakamakon tarin basukan da suka kai miliyoyin Naira kamar yadda rahotanni ke cewa.

Kazalika wasu rahotannin na cewa, akwai wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu, inda sansanin sojin ya amince ya rika biyan Naira miliyan 60 ga ma’aikatan lantarkin a duk wata domin samun wutar akalla sa’o’i 10 zuwa 12 a kowacce rana a sansanin.

Yanzu haka sojojin suk yi ƙorafin cewa, rashin samun lantarkin na barazana ga ayyukansu na samar da tsaro.

An ce sojojin sun ƙaddamar da harin ne kan ofishin rarraba lantarkin da misalin ƙarfe 7 da minti 40 na safiyar wannan Alhamis ƙarkashin jagorancin wata soja mace, inda suka rika dukan ma’aikatan da kuma duk wanda suka samu a harabar ofishin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here