‘Yan bindiga sun kashe mutane 3 tare da sace 12 a Kaduna

0
94

Rahotanni daga jihar Kaduna sun tabbatar da yadda wani gungun ‘yan bindiga da suka farmaki garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna  suka kashe wani sufeton dan sanda tare da mutane 3.

Shaidun gani da ido da ke tabbatarwa faruwar harin, sun ce da misalin karfe 7:30 na daren asabar din karshen makon jiya ne, ‘yan bindigar suka farmaki yankin Hayin Gada da ke garin Damari a mazabar Kazage tare da sace mutane 12 baya ga kashe wasu 3.

A cewar rahotannin cikin wadanda ‘yan bindigar suka kashe har da Sanusi Zubairu da kuma Kabiru Zubairu yayinda kuma suka fasa shagunan jama’a tare da sace tarin kayaki.

Tuni dai masarautar Birni-Gwari ta tabbatar da faruwar harin a yau talata, inda ta ce akwai kuma wani hari na daban da ya hallaka mutum guda yayinda ‘yan bindigar suka sace wasu mutum 6 akan babban titin yankin.

Haka zalika ‘yan bindigar sun kuma kashe wasu mutum 4 a titin Dajin jangali baya ga sace mashina masu kafa biyu kirar Bajaj guda 3 daga manoma a yankin kamfanin Doka.