Shalkwatar tsaron ƙasa tace a cikin mako daya jami’an ta sun kashe yan ta’adda 92 da kama 111 sannan suka kubutar da mutanen da aka yi garkuwa dasu 75.
Daraktan sashin yada labarai na shalkwatar Manjo Janar Markus Kangye, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis.
Yace sojojin sun kwato makamai 117, da sinkin alburusai 2,929.
Makaman da aka kwato sun hadar da AK-47 guda 58, da bindugun gargajiya 21.
Kangye, ya kara da cewa jami’an Sojin dake atisayen tsaftace yankin Neja Delta, sun bankaɗo danyen man fetur da aka sace Lita 452,396, da guma gas da aka tace lita 224,175, sai fetur Lita 1,920.