Gwamnatin Kano ta fara tantance ma’aikatan shara

0
32

 

Gwamnatin jihar Kano ta fara tantance ma’aikatan shara su 2,369 don biyan su albashin da aka jima ba’a biya su ba tsawon watanni 9.

Ma’aikatar Muhalli ta jihar ce ke gudanar da tantance ma’aikatan.

DAILY NIGERIAN, ta rawaito cewa a kwanakin baya ne gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da fitar da kudade don biyan ma’aikatan albashin su na watanni 9 da suke bin gwamnatin.

A wata sanarwa da ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano ta fitar a shafin ta na facebook, ta ce Kwamishinan Ma’aikatar Dakta Dahir M. Hashim, ne ya bayar da umarnin tantance rukunin farko na ma’aikatan su 1,000.

Sanarwar ta ce duk waÉ—anda abun ya shafa su tuntubi jami’o’in su na Æ™ananan hukumomi domin karÉ“ar bayanai akan ranar da za a tantance su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here