Kwamitin majalisar dattawa ya nemi a dakatar da Sanata Natasha tsawon watanni 6, biyo bayan dambarwar dake tsakanin ta da shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio.
Tashar talbijin ta Arise, ce ta rawaito labarin a yau Alhamis.
Tunda farko dai Natasha ta zargi shugaban majalisar da yunkurin yin lalata da ita.
Idan za’a iya tunawa dai a jiya Laraba wata kotun tarayya dake Abuja ta dakatar da majalisar dattawa daga daukar matakin ladabtawa akan Natasha.