Sheikh Sa’eedu Hassan Jingir ya rasu

0
53

Fitaccen malamin Islama na Kungiyar Izala Sheikh Sa’eedu Hassan Jingir ya rasu. 

Sheikh Sa’eedu Hassan Jingir shine mataimakin shugaban Ƙungiyar Izala dake  ƙarƙashin jagoranci Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir.

Ya rasu a gidansa dake Jos bayan fama da jinya ta tsawon lokaci.

Anjima kaɗan ake sa ran za’a yi jana’izar sa a gidansa dake Anguwar Rimi a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here