Rundunar tsaron al’umma ta farin kaya Civil Defence, ta sanar da cewa nan gaba kadan zata fara daukar sabbin ma’aikata a cikin wannan shekara ta 2025.
Kwamandan rundunar NSCDC na kasa Ahmad Audi, ne ya bayyana hakan a yau Laraba lokacin da yake kaddamar da bude ofishin rundunar a Bwari, dake birnin tarayya Abuja.
Yace rundunar su ta samu sahalewa daga shugaban kasa akan daukar matasan Najeriya aiki, inda yace zasu sanar da al’umma lokacin fara daukar sabbin ma’aikata
Audi, ya yabawa shugaban kasa Tinubu, bisa amincewar da yayi a dauki sabbin jami’an rundunar ta NSCDC.