Gwamnan Rivers ya bawa rundunar sojin sama kyautar jirgi

0
73

Gwamnatin jihar Rivers ta bawa rundunar sojin sama ta kasa tallafin jirgi mai saukar Ungulu.

Gwamnan jihar Siminalaya Fubara, ne ya miƙa kyautar jirgin lokacin gudanar da bikin bayar da kyautar yau a birnin Fatakwal.

Fubara ya kara da cewa kyautar bata da wata alaka da siyasa sai dai don inganta tsaro.Shugaban rundunar sojin sama ta kasa AVM Hassan Bala Abubakar, ne ya karbi kyautar a madadin daukacin ma’aikatan rundunar.

Yace jirgin zai taimaka wajen samar da tsaro musamman a jihar Rivers da yankin Neja Delta baki daya.

Taron ya samu halartar shugabannin rundunar sojin sama, jami’an gwamnatin jihar Rivers da masu sarautar gargajiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here