Shugaban kasar Amurka Trump, yace yana fuskantar kasar Rasha na son samar da yarjejeniyar zaman lafiya a yakin ta da kasar Ukraine, yana mai cewa yana da tabbaci akan hakan.
Donald Trump, ya sanar da hakan lokacin da yake yin jawabi ga majalisar dokokin Amurka a karon farko bayan sake zabar sa a matsayin shugaban Amurka.
Shugaban na Amurka yace a safiyar yau shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya turo masa wasikar dake cewa shima yana son a samar da zaman lafiya tsakanin sa da Rasha.
Zelensky ya aike da wasikar bayan da Amurka ta dakatar da tallafin da take bawa sojojin Ukraine.