Dan shekara 20 ya kashe mahafiyar sa da Tabarya

0
67

Jami’an yan sanda sun kama wani matashi dan shekaru 20 mai suna Safiyanu Dalhatu, bisa zargin sa da hallaka mahaifiyar sa da Tabarya a jihar Bauchi.

Kakakin rundunar yan sandan Bauchi CSP, Ahmed Wakili, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa, yana mai cewa lamarin ya faru a ranar 24, ga watan Fabrairun daya gabata.

:::Kotun Kano ta tura yan TikTok gidan yari

Yace matashin ya kashe babar tasa a unguwar Abujan Kwata dake jihar Bauchi.

Sanarwar tace ana zargin Safiyanu, da yiwa babar sa duka da tabarya har sai da ta mutu.

Safiyanu ya yiwa mahaifiyar tasa mai suna Salama Abdullahi yar shekara 40 munanan raunuka, kafin mutuwar tata.

Wakili, yace jamia’n yan sanda ne suka kai mamaciyar asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa, inda a nan ne aka tabbatar da mutuwar Salama. Sannan yace za’a mika wanda ake zargi da kisan zuwa kotu bayan kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here