DSS sun chafke wani soja da yake siyarwa da ‘yan ta’adda makamai a Abuja

0
108

Wani soja da ke Birnin Tarayya Abuja, ya shiga komar Hukumar Tsaro ta DSS bisa zarginsa da sayar da bindiga ga masu garkuwa da mutane.

Wani jami’in tsaron sa kai ya shaida wa Aminiya cewa, ofishin DSS din da ke Gwagwalada ne suka nemi tallafin jami’an tsaron Zuba, wajen kamo wanda ake zargin.

Majiyar ta ce, “An gano wanda ake zargin a baya ma ya taba sayar musu da bindigar kan N300,000.

“Sai na biyu kuma da ya sayar kan N200,00, wanda ’yan Bindigar suka biya, amma ya gaza kawo musu,” a cewar majiyar tamu.

Haka kuma majiyar ta ci gaba da cewa, bayan da DSS din suka samu nasarar kamo masu satar mutanen, sun sanar da su batun.

“Shi ne aka shirya sintiri na musamman domin kama shi da kuma tabbatar da gaskiyar lamarin.

“Sai aka tuntube shi a matsayin masu satar mutane ne ke son sayen wata bindigar kirar AK-47, kan Naira miliyan uku.

“Ya bayyana mana inda za mu hadu mu karba, muka amince. Yana zuwa da bindigar kuwa aka kama shi.

“Bindigar cike take da harsasai kuma a motarsa ma an samu wasu albarusan guda 30.

“Daga nan muka kai shi ofishinmu, sannan muka mika shi ga DSS din,” inji majiyar.

Kazalika Wakilinmu ya gano cewa Rundunar Sojoji daga shalkwatasu ta Abuja, sun je ofishin Jami’an Tsaron sa kan da ke Zuban, in da suka dauki bayaninsu kan lamarin a rubuce.

AMINIYA