Mijin Natasha yayi korafi akan Akpabio

0
35

Mai gidan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan ya magantu game da rikicin da ke tsakanin matarsa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Mijin, wanda basarake ne a yankin Neja Delta ya ce matarsa tayi masa bayani a baya lokacin da Akpabio ya ci zarafinta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Emmanuel Oritsejolomi, yace tun a lokacin da kansa ya samu Akpabio, inda ya nemi a rika mutunta matar tasa, musamman saboda abotar dake tsakanin mijin da Akpabio, kuma a cewar sa an warware duk wata matsala a lokacin cikin mutuntaka.

Yace duk da haka Akpabio ya cigaba da cin zarafin Natasha saboda tana sanar da shi duk abubuwan dake faruwa tsakanin su.

Basaraken yace yana da yarda akan matar sa saboda auren soyayya suka yi, tare da cewa a yanzu Natasha tafi komai muhimmanci a wajen sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here