Miji ya kashe matar sa saboda abincin shan ruwan Azumi

0
70

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama wani magidanci mai suna Alhaji Nuru Isah kan zargin sa da kisan matar sa Wasila Abdullahi, a ranar asabar data gabata.

Wasu rahotanni sun nuna cewa rikici ya barke tsakanin ma’auratan a gidan su dake kusa da makarantar GG Bauchi a unguwar Fadaman Mada, dangane da yadda za a raba kayan abinci da kayan marmari don yin buda baki a Azumin watan Ramadan. 

Wani makwabcin inda lamarin ya faru ya ce takaddamar miji da matar ta rikide zuwa fada, inda Alhaji Nuru Isah ya dauki sanda ya buge matarsa, hakan kuma yasa ta sume.

An tabbatar da mutuwar ta bayan kai ta asibitin koyarwa na Jami’ar ATBU.

Alhaji Nuru ya kasance mai shekaru 50, ita kuwa matar tasa wasila tana da shekaru 24 a duniya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakili, ya tabbatar da kisan, tare da tsare wanda ake zargin aikata kisan, don cigaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here