Sarkin Sasa ya rasu yana da shekaru 125

0
87

Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin Katsina, ya rasu yana da shekaru 125, a duniya.

Daya daga cikin ‘ya’yan sa Alhaji Kasim Ado Yaro, ne ya sanar da rasuwar a jiya Asabar.

Kafin rasuwar sa shine shugaban majalisar Sarakunan Hausawa a jihohin Kudancin Najeriya 17.

ÆŠan nasa ya bayyana Marigayiya a matsayin mai gaskiya dattako da rikon amana kamar yadda ya bayyana a cikin wata sanarwa daya fitar.

Tuni masu rike da sarautun gargajiya suka fara mika sakon ta’aziyyar su ga yan uwa, iyalai da abokan Sarkin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here