Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, yace ba kiyayya ce tasa yake kalubalantar manufofin gwamnatin shugaban kasa Tinubu ba, sai dai yana goyon bayan duk wani tsari na cigaba, gaskiya da adalci.
Gwamnan ya sanar da hakan a karamar hukumar Gamawa dake jihar Bauchi, lokacin kaddamar da aikin tallafawa manoma a yau Asabar.
Yace mafi yawancin mutane suna yi masa kallon mai yin rigima da shugaban Kasa, inda yace ba haka abun yake ba, sannan yayi nuni da cewa zai yi biyayya ga duk wani shirin inganta rayuwar al’umma da walwalar su.
Gwamna Bala Muhammad, yace ba batun siyasa ne ya tara su a karamar hukumar Gamawa ba, illa aikin hadin kai da kuma inganta noma da al’umma.