Gobara ta ƙone shaguna a kasuwar Kara

0
28

Tashin wata mummunar gobara yayi sanadiyyar konewar shaguna da dama a kasuwar Kara dake jihar Sokoto.

Zuwa yanzu jami’an hukumar kashe gobara na cigaba da kokarin kashe wutar da ba’a gano musabbabin tashin ta ba.

An bayar da rahoton cewa an tafka babbar asara a tashin gobarar data cinye shaguna da dama.

Yayin kashe gobarar an samu masu saka idanu dangane da bata gari masu kokarin sace dukiyar al’umma in aka samu irin wannan iftila’i.

Gobarar ta tashi a farkon awannin wannan rana ta Asabar, inda ta rika yin saurin ciyo shaguna, duk da cewa mutanen dake kasuwanci a wajen suna ta kokarin kwashe kayayyakin su.

Zuwa yanzu dai ba’a san adadin dukiyar da akayi asara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here