EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Abia akan zargin sace Naira biliyan 60.85

0
38

EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta kasa, ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia Theodore Orji, da wasu mutane 4, akan zargin su da sace Naira biliyan 60.85, mallakin jihar a zamanin mulkin sa.

An gurfanar da su a gaban babbar kotun jihar Abia dake Umuahia, karkashin jagorancin mai shari’a Lilian Abai.

An gurfanar da su akan zargin su da aikata manyan laifuka 16, da suka kunshi yin amfani da kudin jihar Abia har Naira biliyan 60.85, ta hanyar da bata dace ba

Mutanen da aka shigar da karar sune Theodore Ahamefule Orji, Engr. Chinedum Orji, Dr. Phillip Nto, Onwumene King Obioma, da kuma Romanus K. Madu.

Ana sa ran nan gaba kadan za’a sanar da lokacin fara gudanar da shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here