Shugaban majalisar Dattawa yaso yin lalata dani—Natasha

0
98

Natasha Akpoti-Uduaghan, Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, ta zargi shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, da neman yin lalata da ita.

Natasha, tace kin amincewar data yiwa Akpabio ya lalata ta shine dalilin da yasa ake samun tankiya tsakanin ta dashi.

Akpoti, ta yi wannan zargin yayin wata hira da talbijin ta Arise a yau Juma’a.

A makon daya gabata ne aka samu rashin jituwa tsakanin Akpabio da Natasha, a zauren majalisar wanda hakan ya janyo cece-kuce da hatsaniya a zauren majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here