Yan ta’adda sun kashe manoma da sace shanu a Neja

0
29

Yan ta’adda sun kashe manoma da sace wasu a kauyen Kagara dake mazabar Bassa a karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Akalla manoma 9 yan ta’addan suka halaka sannan suka yi awon gaba wasu 6, bayan sace shanu masu yawa.

Daily trust, ta rawaito cewa mutanen sun kai harin a cikin daren Larabar data gabata, inda suka rika bi gida-gida suna kashe mutanen.

Mutane 6 da aka sace sun kasance mazauna yankin Farin-Doki, dake Shiroro, wanda su kuma na Kagara aka yi musu kisan gilla.

Wata Majiya tace an samu gawarwaki 9 kuma za’a iya samun karin wasu mutanen da aka kashe yayin harin.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Neja Wasiu Abiodun, yace zai yi karin haske akan harin bayan ya kammala tattara bayanai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here