Gwamnatin Kano ta nemi shugaban kasa Tinubu, ya bawa Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, umarnin ficewa daga jihar, yayin da gwmanatin tace bata son a haifar mata da rashin zaman lafiya akan maganar rikicin masarautar Kano.
Gwamnatin ta bakin mataimakin gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo, yace kamata yayi shugaban kasar ya kai Aminu Ado, jihar Lagos sannan ya naÉ—a shi sarautar can.
Mataimakin gwamnan ya bayyana haka a matsayin mayar da martani kan kariyar da jami’an tsaro ke bai wa sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero a mazaunin sa da ke gidan Sarki na Nassarawa Nassarawa.