Gwamnatin tarayya, jihohi da kananun hukumomin kasar nan sun raba Naira Naira triliyan 1.703, a watan Junairu.
An raba kudaden ne bayan tattara su daga asusun gwamnatin tarayya.
A cikin watan na Junairu 2025, gwmanatin ta tattara kudin shigar da yakai Naira triliyan 2.641.
A yau Alhamis ne aka sanar da rabon kudaden bayan gudanar taron kwamitin asusun tattarawa da rabon arziƙin kasa daya gudana a birnin tarayya Abuja.
A cikin kudin da aka raba gwmanatin tarayya ta karbi Naira biliyan 552.591, sai jihohi sun karbi Naira 590.614, yayin da kananun hukumomi aka basu Naira biliyan 434.567.