Yan bindiga sun sace yan mata 4 a wajen kwanan su na jami’a

0
69

Wasu yan bindigar da ba’a sani ba sun yi garkuwa da yan mata 4 masu karatu a jami’ar Joseph Sarwan Tarka, dake makurdi.

Masu garkuwar sun sace É—aliban a daren ranar Talata a wajen kwanan su, wanda hakan ya tilastawa hukumar gudanarwar jami’ar rufe koyarwa zuwa mako daya kafin komai ya daidaita.

Wadanda aka sace sune Emmanuella, Fola, Susan, da Ella.

Jami’ar tace yan bindiga 5 ne suka sace É—aliban da misalin karfe 8:30, na dare, sannan suka yi gaba dasu.

Bayan sace yan matan sauran dalibai sun taru tare da fara yin zanga zangar neman a dauki matakin ceto yan uwan karatun su.

Haka ne yasa maga takardan makarantan jami’ar Dr. John David, yin ala wadai da sace É—aliban, yana mai cewa jami’an tsaro suna yin bakin kakakin su wajen ceto daliban, da hadin gwuiwar gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here