Yan bindiga sun bayar da umarnin bude kasuwannin da aka rufe

0
82
ISWAP BOKO HARAM
Boko Haram ISWAP

Yan bindigar da aka yi yarjejeniyar zaman lafiya dasu a jihohin Kaduna Katsina da Neja, sun bayar da hakuri ga al’umma sakamakon karya yarjejeniyar da suka yi a baya tare da kai hare hare.

Yan bindigar sun bayyana hakan a jiya Laraba lokacin da al’ummar yankunan da aka yi yarjejeniyar suka sake zama da maharan don jaddada samun daidaituwa a tsakanin su saboda hare hare haren da suka kai duk da cewa an yi sulhu da hujjar cewa ba zasu farmaki mutane ba. A yayin zaman maharan sun fadi wasu dalilan da suka sanya su kai hari duk da yarjejeniyar.

A yayin tattaunawar maharan sun bayar da damar bude kasuwannin da suka tilasta rufewa, inda suka ce za’a iya cigaba da kasuwanci babu matsala tunda an jaddada yarjejeniyar zaman lafiyar, tare da neman a yafe musu laifukan da suka aikata a baya.

Daya daga cikin mutanen Birnin Gwari, dake Kaduna Zubairu Abdul’rauf, yace an samu fahimta da yan bindigar.

Yankunan da akayi zaman sulhun sun hadar da Birnin Gwari na jihar Kaduna da Dugun Mu’azu na Æ™aramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina da wasu yankunan jihar Neja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here