Kungiyoyin damfara na kasashen waje sun fara koyawa matasan Najeriya laifuka—EFCC

0
34

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa  EFCC, Ola Olukoyede, ya ce kungiyoyin damfara na kasashen waje suna shigo da makamai cikin Najeriya ta hanyar amfani da kudaden internet wato (cryptocurrency) a matsayin hanyar biyan kudin makaman.

Olukoyede ya yi wannan jawabin a ranar Laraba yayin da yake karbar bakuncin mahalarta kwas din koyar da aikin leken asiri na Cibiyar Nazarin Tsaro ta Kasa (NISS) dake Abuja.

Shugaban Cibiyar (NISS) Hyginus Ngele, ne ya jagoranci zuwa wajen shugaban hukumar ta EFCC.

Olukoyede, yace kungiyoyin damfarar kasashen waje suna nan suna kirkirar gungun bata gari a cikin biranen Najeriya tare da koyawa matasa damfara da zamba a yanar gizo.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan kasashen waje da aka kama bisa laifin zamba a Najeriya, masu laifi ne da kuma wadanda aka yankewa hukunci a kasashensu. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here