Kotu ta bayar da belin Farfesa Usman Yusuf bayan shafe kwanaki 24 a hannun jami‘an tsaro bisa zargen-zargen aikata ba daidai ba da hukumar EFCC.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ce ta kama Farfesan kwanakin baya a gidan sa dake Abuja, wanda bayan dan lokaci ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin sa da aikata laifi a wata kungiya.
Farfesa Usman Yusuf, ya kasance daya daga cikin masu kalubalantar manufofin gwamnatiin Tinubu, da ake ganin hakan na daga cikin abubuwan da suka kara sanyawa aka kama shi.