Shugaban kasa Bola Tinubu, ya sanar da ninka kason da gwamnatin tarayya aikewa jihohi a kowanne wata sau uku.
Yace an kara kason da ake aikewa jihohin daga asusun gwamnatin tarayya saboda cire tallafin man fetur.
:::Kuwait zata taimakawa adadi mai yawa na yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya
Tinubu, ya sanar da hakan a daren Talata, lokacin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na APC, daya gudanar a fadar gwamnatin tarayya, yana mai cewa cire tallafin man fetur shine alkairi ga Najeriya, bisa hujjar sa ta cewa rashin cire tallafin zai iya rushe kasar baki daya.
A cewar sa cire tallafin ya bayar da damar yin ayyukan raya kasa kamar samar da shirin bayar da rancen kudin karatu, da kuma tanadar kudaden da za’a iya bawa kowacce karamar hukumar kasar don yin ayyukan cigaban al’umma, da kuma ninka kudaden da ake bawa jihohi har sau uku.