Cutar Lassa ta kashe mutane 80 

0
39

Akalla mutane 80 cutar zazzabin Lassa ta kashe a Najeriya tsakanin 3 zuwa 9 ga watan Fabrairu 2025.

Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC, ce ta sanar da hakan a shafin ta bayan fitar da rahoton alkaluman da suka shafi cutar a baya bayan nan.

NCDC tace an samu raguwar adadin mutanen da ke kamuwa da cutar ta Lassa in aka kwatanta da baya.

Jihohin da aka samu sabbin masu fama da cutar sun kunshi Bauchi, Ondo, Taraba, Edo, Gombe, Kogi, da Ebonyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here