0
49

Shugaban Nijar ya nemi yan kasuwa su rage farashin kayan abinci saboda Azumi

Shugaban Nijar na mulkin soji Janar Abdourahamane Tchiani ya buƙaci jami’an gwamnatinsa da su wayar da kan manyan ’yan kasuwa akan su guji tsawwala farashin kayan abinci kuma su tabbatar an samu wadatuwar kayan abincin a lokacin watan azumin Ramadan.

Janar Tiani ya bayyana haka yayin wani zama na musamman kan shirye-shiryen watan Ramadan da ya yi da majalisar ministocin kasar a ƙarshen mako.

Wannan kira da Janar Tiani ya yi yana zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin tabbatar da cewa mutane masu ƙaramin ƙarfi suna samun muhimman abubuwan da suke buƙata ba tare da fuskantar wahala ba.

Ita ma gwamnatin a nata ɓangaren ta jaddada cewa za ta tabbatar da wadatuwar kayayyakin buƙatar yau da kullum a faɗin ƙasar.

Sakamakon haka ne ya sa gwamnatin ta fara ɗaukar mataki inda aka tura dakarun ƙasar iyakar ƙasar da Burkina Faso inda suke raka dubban manyan motoci da suke ɗauke da abinci zuwa cikin ƙasar, a cewar majalisar wannan mataki ya taimaka wajen wadatuwar abincin da ake matuƙar buƙata a lokacin watan Ramadan.

Sannan majalisar ta jinjina kan wani mataki da ƙasar ta ɗauka na dakatar da fitar da wasu muhimman kayan abinci daga cikin ƙasar zuwa ƙasashe maƙwabta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here