NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila, Ali Madaki, da karin wasu yan majalisa

0
76

Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta dauki matakin dakatar da wasu daga cikin yan majalisun dokokin kasa na jam’iyyar bisa zargin su da cin amana.

Shugaban jam’iyyar na jihar Kano Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a jihar Kano ranar litinin.

Yace cikin wadanda aka dakatar akwai Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, dake wakiltar kudancin Kano, sai Ali Madaki na karamar hukumar Dala, da Abdullahi Sani Rogo, sai Kabiru Alhassan Rurum.

Dungurawa, yace basu ji dadin wasu abubuwan da yayan jam’iyyar suka aikata ba a baya bayan nan wanda haka ne yasa aka dauki matakin ladabtawar akan su.

Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, ya kara da cewa duk da basu damar zama yan majalisa a karkashin jam’iyyar amma suna aikata abubuwan da suka saba da dokokin NNPP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here